Kakakin Majalisar dokokin jihar Sokoto, Aminu Muhammad Achida ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP.
Achida ya gabatar da wasikar sauya shekarsa ga Majalisar yayin zaman Majalisar a ranar Alhamis 14 ga watan Afrilu.
Dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Wammako 2, Murtala Bello Maigona shi ma ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.