Da duminsa: Yan fashi da makami sun kai hari a gidan rediyon FM ana tsakar watsa shirye-shirye kai tsaye


Gungun wasu Yan fashi da makami sun farmaki wani gidan rediyon Fresh FM mallakin fitaccen mawakin nan mai suna Yinka Ayefele da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo da safiyar Lahadi, 10 ga watan Afrilu. Shafin Jaridar isyaku.com ya wallafa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, ‘yan fashin sun kai farmaki gidan rediyon ne a lokacin da ake watsa shirye-shiryen kai tsaye tare da korar ma’aikatan da ke aikin, kuma suka kwashe kwamfutoci da wayoyi da sauran abubuwan masu amfani.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na safe an kuma gano cewa babu wanda ya jikkata. Daya daga cikin ma’aikatan gidan rediyon, Kenny Ogunmiloro ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa; 

"Babu inda ake samun kwanciyar hankali, hatta gidajen rediyon ma ba su tsira daga rashin tsaro a kasar nan, wasu mutane 3 dauke da makamai sun farmaki gidan rediyonmu da safiyar yau da misalin karfe 6:15 na safe. An tafi da wayoyi, kwamfutar tafi-da-gidanka, katunan ATM, da na'urori amma babu wanda ya ji rauni. Wannan abin bakin ciki ne".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN