Da duminsa: NDLEA ta kama attajirin da ya kulla harkallar kwaya da Abba Kyari, duba ka kani


Hukumar NDLEA ta samu nasarar kame Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, wani attajirin da ake zargin yana da hannu a harkallar safarar miyagun kwayoyi ta DCP Abba Kyari da tawagarsa.

Sanarwar da NDLEA ta fitar ta bayyana cewa Afam na da hannu dumu-dumu a harkallar shigo da miyagun kwayoyi na N3bn da ke da alaka da Abba Kyari.

Bayan shafe watanni ana sa ido akansa, an kama Mista Ukatu wanda shi ne shugaban Kamfanin Mallinson Group of Companies, a cikin jirgin da zai je Abuja daga filin jirgin saman Legas, Ikeja a ranar Laraba 13 ga Afrilu.

Hukumar ta ce Afam babban mai shigo da miyagun haramtattun kayayyaki ne, wadanda suka hada da kwayoyin Tramadol da dai sauransu.

A cewar hukumar ta NDLEA, wanda ake zargin yana tafiyar da kamfanonin harhada magunguna da yake amfani da su wajen fakewa da shigo da kwayoyin ba bisa ka’ida ba cikin Najeriya, baya ga cewa ya mallaki asusun banki kusan 103 da aka fi amfani da su wajen badakalar kudade.

Hukumar ta tabbar da batun kamun ne ta hanyar wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin, 25 ga Afrilu.

A wani labarin, hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayyana yadda tayi ram da wani Pascal Okolo bayan ta kama shi dumu-dumu da hodar iblis.

A wata takarda da kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi a shafinsu na Twitter, ya bayyana yadda aka boye hodar iblis mai nauyin 4.1 kg a jakunkunan shayi.

Ya ce, an ga hakan ne yayin bincikar kayansa na jirgin saman da ya iso Najeriya daga Sao Paulo ta Doha a 17 ga watan Afirilu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN