A watan Ramadan: Sojin Isra'ila sun kai wa Musulmi farmaki a cikin Masallacin Qudus


Wani rahoton jaridar Arab News ya ce, jami'an tsaron Isra'ila sun shiga harabar masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus da asuba ranar Juma'a a daidai lokacin da dubban Falasdinawa suka taru domin gudanar da sallah a cikin watan Ramadan
.

Lamarin dai ya haifar da artabu, inda ma'aikatan lafiya suka ce akalla Falasdinawa 117 ne suka jikkata. Legit ta ruwaito.

Isra'ila ta ce dakarunta sun shiga masallacin ne domin kwashe wasu duwatsu da aka tara da nufin tada hankali, inji rahoton GulfNews.

Masallacin Al-Aqsa mai tsarki ya kasance cibiyar tarzoma tsakanin Isra'ila da Falasdinu, kuma an sha samun tashe-tashen hankula a lokuta masu tsawo.

Rikici a wurin a bara ya haifar da yakin kwanaki 11 da mayakan Hamas a zirin Gaza.

Rikicin ya zo ne a wani lokaci na musamman; Ramadan na wannan shekara ya zo daidai da Idin Ketarawa na Passover, babban hutun Yahudawa na mako guda da ke farawa ranar Juma'a da faduwar rana, da kuma mako mai tsarki na Kirista, Easter.

Ana sa ran bukukuwan za su kawo dubun-dubatar jama'a zuwa cikin Tsohon Birnin Kudus, gida ga manyan wuraren masu tsarki ga dukan addinai uku.

Bidiyo ya nuna yadda jami'an tsaron Isra'ila ke cin zarafin Musulmai

Wani bidiyo da ke yawo a yanar gizo ya nuna yadda Falasdinawan ke jifa da duwatsu, yayin da 'yan sanda ke harba barkwanon tsohuwa a kan jama'ar da ke kewaye da masallacin.

Wasu bidiyon kuma sun nuna yadda masu ibada ke kare kansu a cikin masallacin yayin da hayakin barkwanon tsohuwa ya turnuke masallacin.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce ta yi jinyar mutane 117 sakamakon farmakin na jami'an tsaron Isra'ila.

Red Crescent ta ce da dama daga cikin Falasdinawa sun samu raunuka daga harsashin roba, barkwanon tsohuwa da kuma duka su da sanduna. Hukumar agajin ta ce an harbe daya daga cikin masu gadin wurin da harsashin roba a ido.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN