EFCC ta kama matar wani Gwamna


Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta kama Eberechukwu, matar tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano.

Kamar yadda rahoton Punch  ya ruwaito, Mrs Obiano, wadda aka yi ta bincike a kan zargin zamba, a halin yanzu tana hannun hukumar a Abuja.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce bai da masaniya kan kamun da aka yi wa matar tsohon Gwamnan, ya kuma yi alkawarin gano bakin zaren hakan amma bai yi Karin bayani ba.

Wannan sabon al’amari dai na zuwa ne kimanin wata guda bayan da aka kama mijin nata a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, a lokacin da yake shirin shiga jirgin sama zuwa birnin Houston na kasar Amurka, sa’o’i kadan bayan mika mulki ga magajinsa, Soludo.

Washegari aka kai shi Abuja aka yi masa tambayoyi kan zargin almubazzaranci da dukiyar al’umma da suka hada da, Naira biliyan 5 da Sure-P da kuma Naira biliyan 37 na tsaro da aka cire a cikin baitulmalin kudin jiharsa lokacin mulkinsa. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN