Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kashe dogarin Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi shi kuma ya ketare rijiya da baya a farmakin garin Kanya, sun kashe jami'an tsaro 19


Yan bindiga sun kashe Kwamandan dogarawan tsaron Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ASP Idris Umar Libata a garin Kanya, lokacin wani gumurzu da ya gudana tsakanin Yan bindiga da jami'an tsaro ranar Talata 8 ga watan Maris 2022. Shafin labarai na isyaku.com ya labarta.

Wannan Yana zuwa ne bayan Yan bindigan sun kashe Yan sa kai guda 63 a wani kwanton bauna da suka yi masu a yankin kudancin Masarautar Zuru ranar Lahadi 7 ga watan Maris.

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ya ketare rijiya da baya

Rahotanni na cewa Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe Dabai ya auna arziki bayan an rutsa da tawagarshi a farmakin da Yan bindigan suka kaddamar a garin Kanya.

Mun samo cewa Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ya tsira a farmakin da ya rutsa da shi, sai dai Kwamandan dogarawan tsaron shi ya rasa ransa wajen yin harba harba da Yan bindigan domin kare Mataimakin Gwamna.

Kazalika majiyarmu ta ce lamarin ya faru ne tsakanin Magariba zuwa isha'i a daidai wani waje da ke da duhun gandun itatuwa da aka fi sani da Forest wanda ke kudu daga garin Kanya kusa da sabon Asibitin da Sanata Bala Ib'n Na Allah ya gina a garin Kanya.

Yan bindigan sun kone motar soji tare da raunata soji 8

Sakamakon farmakin da Yan bindigan suka kaddamar a garin Kanya ranar Talata, wanda suka fara daga kusan karfe 5 na yamma kamar yadda wata majiya ta labarta, soji sun fuskanci yan bindigan, kuma aka yi ta yin artabu tun daga wannan lokaci har zuwa duhun dare.

Yan bindigan sun kone motar soji guda daya, suka kuma raunata soji 8. Sai dai majiyarmu ta ce soji sun yi wa Yan bindigan mumunar barna tare da kashe su da yawa. Kazalika majiyar ta ce Yan bindigan sukan dauke gawakin mutanensu da aka kashe me, su dora su a babura su shiga daji da su.

Lamari da ya sa aka kasa samun adadin yawan Yan bindigan da soji suka halaka a gumurzun na ranar Talata.

Ana fargaban cewa an kashe soji 19 da dansandan kwantar da tarzoma guda daya.

Da safiyar ranar Laraba, an ga gawakin soji 15 a wajen da aka yi artabu tsakanin Yan bindigan da soji da suka jajirce suka rasa rayukansu wajen kare kasar Kanya a artabu da aka yi cikin dare. Sai dai wata majiya ta ce ana fargaban cewa 3 daga cikin soji 8 da suka sami rauni sakamakon artabu da Yan bindigan da suke jinya a asibiti sun mutu kafin safiyar Laraba.

Wanda hakan ya kawo jimillar soji da suka mutu zuwa 18, da kuma Kwamandan dogarawan tsaron Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi, wanda dansandan kwantar da tarzoma ne. Jimilla jami'an tsaro 19 sun mutu a wannan farmaki a cewa majiyar.

Sarkin grin Kanya lokacin artabu da Yan bindiga

Ana zargin cewa Sarkin Kanya ya bace cikin dare lokcin da artabu ya yi tsanani tsakanin soji da Yan bindiga, domin dai ba a ganshi cikin dare ba sai da safe ranar Laraba ya bayyana a cewar wata majiya.

Yan bindiga sun shiga gidaje suka kwace wayoyin salula da kayan abinci

A cikin duhun dare ranar Talata, bayan gumurzu, Yan bindiga sun shiga wasu gidaje suka kwace wayoyin salula na jama'a. Sun kuma fasa shagunan jama'a suka kwashe cimaka da abin da suka gan dama tare da kora shanaye da suka iya korawa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN