Yadda aka yi Janaizar Kwamandan dogarawan Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi da Yan bindiga suka kashe a Masarautar Zuru (Hotuna)An gudanar da Sallar Jana"izar ASP Idris Umar Libata, Kwamandan dogarawan Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi.

An gudanar da jana'izarsa ne a harabar dakin ajiye gawaki da ke Asibitin Sir Yahaya da ke garin Birnin kebbi da karfe 5:30 na yamma, daga bisani aka wuce da gawarsa zuwa Makabarta domin birneta.

Manyan ma'aikatan Gwamnati sashen tsaro na jihar Kebbi da wasu manyan yansanda, da sauran jama'a sun halarci wannan Jana'iza tare da Yan uwa da abokan Marigayi Idris Umar.

Da karfe 3: 30 na rana motocin Bas suka iso garin Birnin kebbi dauke da gawakin jami'an tsaron da Yan bindiga suka kashe a garin Kanya da ke karamar hukumar Danko Wasagu a Masarautar Zuru ranar Talata. 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN