Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, kamfanin jiragen sama na Air Peace ya dakatar da ayyukansa zuwa filin jirgin sama na Kaduna.
Wata majiya ta alakanta faruwar lamarin ga harin da aka kai a kusa da filin jirgin Kaduna a karshen makon jiya.
Idan baku manta ba, an ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga suka bindige wani mai gadi da ke aiki a hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya a ranar Asabar.
Sojoji sun yi artabu da ‘yan ta’addan, lamarin da ya janyo tsaikon tashin jirgin sama na Azman da ke kan hanyarsa ta zuwa Legas.
A ranar Talata ne Azman ya sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragensa zuwa Kaduna har sai baba ta gani saboda rashin tsaro a yankin.
Bayan sa’o’i kadan ne aka samu labarin dakatar da ayyukan jiragen Air Peace zuwa Kaduna.
Karin bayani na nan tafe...
Source: Legit.ng