Alkali Ijeoma Ojukwu na babbar kutun tarayya da ke zamanta a Maitama a birnin Abuja ta daure Mohammed Sani Zubair har tsawon shekara biyu a Kurkuku. Shafin Jaridar isyaku.com ya samo.
Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren, ya sanar da haka. Ya ce Mr Zubair, yana daya daga cikin gungun madamfara da ke cutar jama'a.
Sanarwar ta ce Mr Zubair ya damfari wani Janar na soji Mai murabus kudi har N180,000,000.
An shafe shekara 4 ana gudanar da shari'ar da ta faro tun 2018. Sai dai Kotu ta ba Mr Zubair zabin biyan tarar N400.000.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI