Ministan yada labarai da al’adun kasa, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana abin da ya jawo gwamnatin APC ta gaza shawo kan wasu matsalolin Najeriya.
Kamar yadda Legit.ng ta samu labari, Lai Mohammed ya yi wannan bayani a lokacin da ya yi magana da ‘yan jarida a ranar Litinin, 28 ga watan Maris 2022.
Ministan labarai da al’adun ya ce har yanzu gwamnatin tarayya ta na fama da wasu daga cikin matsalolin da ta gada daga wajen gwamnatin PDP ne tun 2015.
Lai ya fadawa manema labarai cewa don haka, jam’iyyar hamayya ta PDP ba ta da hurumin da za ta fito, ta na sukar APC da ta ke yin iya bakin kokarinta a yau.
Shekaru 4 sun yi kadan - Lai
Mohammed ya ce jam’iyyar PDP ce ta kashe Najeriya a tsawon shekaru 16 da tayi a kan mulki. Ministan ya ce shekaru hudu ba za su isa a gama gyaran ba.
This Day ta ji Ministan ya na cewa sukar da PDP ta ke yi wa gwamnatin APC tamkar mai amalala ne yake dariya ga mai wanke gadon da ya yi wa sharkaf da fitsari.
Najeriya na shigo da fetur har gobe
Har yanzu Ministan ya na bada uzuri, ya ce gwamnatocin PDP sun amfana lokacin da fetur ya yi tsada a Duniya, amma ba su iya gyara matatun da ake da su ba.
Alhaji Mohammed ya ce a shekarar nan za a bude matatar Dangote, wanda a cewarsa hakan ya nuna yadda gwamnatin Buhari ta ke taimakawa ‘yan kasuwa.
“Gwamnatin PDP ba ta iya gyara matatu ba. Abin da ke faruwa a yau shi ne har yau mu na shigo da mai ne.
“Gwamnatin nan ta kaddamar da karamin matata daya, kuma akwai kananan matatu uku da suke nan tafe.”
“Kamar mutum ne ya yi shekaru 16 ya na barna, kuma ana fatan mu gyara ta’adinsu a cikin shekaru hudu.” - Lai
Legit