Yanzu-yanzu: Matar Abba Kyari ta yanke jiki ta fadi a cikin kotu ( Bidiyo)


Ramatu Kyari, Matar jami'in dan sandan Najeriya da aka dakatar, DCP Abba Kyari, ta yanke jiki ta fadi cikin harabar babbar kotun tarayya dake birnin Abuja.

Matar, sanya da bakin Hijabi ta yanke jiki ta fadi ne lokacin da Alkali Emeka Nwite yayi watsi da bukatar belin Abba Kyari bisa zargin safarar hodar iblis da ake masa.

Matar ta zube kasa ne lokacin da jami'an NDLEA suka tasa keyar Abba Kyari da sauran wadanda ake zargi daga cikin kotun, rahoton Vanguard.

Kamar ta sume, wasu jami'an NDLEA da lauyoyi sukayi gaggawan kwasheta daga kasa kuma suka shigar da ita daya daga cikin ofishohin dake cikin kotu.

Kawo yanzu misalin karfe 11, ana kokarin nema mata abin shaka lokacin da matan da suka rako ta kotu suka cewa tana fama da cutar asma.

Latsa nan ka kalli bidiyo

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=10221191726157847&id=1086336452

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN