Siyasar Kebbi: Ba dan Jarida, Blogger ko dan soshiyal midiya da yan siyasar jihar Kebbi suka martaba da lambar yabo tun 2015


Yan jaridu, masu bayar da labarai na zamani Bloggers, da Yan soshiyal midiya sun taka rawar gani matukar gaske wajen ganin Yan siyasa sun kai ga dare karagar mulki a jihar Kebbi tun daga 2015 har zuwa yau.

Bloggers da yan soshiyal midiya sun fi bayar da gudunmuwa wajen tallata yan siyasa a kafafen sada zumunta. Sakamakon haka suka ceto yan siyasa daga kashe makuddan miliyoyi wajen tallata manufofinsu a wasu kafafen labarai. 

Sai dai akan ba yan soshiyal midiya yan kudi kalilan domin tallata yan siyasa saboda sun jahilci matukar tasirin aikin da suke yi wa yan siyasa na tallata su ba tare da wani ingantaccen ka'ida ko tsari ba.

A jihar Kebbi yanzu haka, yan soshiyal midiya suna korafe-korafen cewa yan siyasa basu kyauta masu ba domin ba abin da suka tsinana masu tun byan sun ci zabe a 2015 har zuwa yau.

Kazalika yan siyasa da suka dare karagar mulkin jama'a a jihar Kebbi tun 2015, sun kasa saka wa yan Jarida, Bloggers, da yan soshiyal midiya ko da ta hanyar karrama su da shirin bayar da kyautar yabo ga wadanda suka fi yin fice da nuna kwazo wajen gudanar da aikinsu domin ganin an kai ga nassarar mataki da yan siyasa suka sami kansu na shugabantar jama'a yanzu haka a jihar Kebbi. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN