Jerin yadda sojoji 18, yan sanda 6 da mutane 76 suka rasa ransu cikin mako guda




Akalla mutum 103 ne suka rasa rayukansu a hannun yan ta'adda a Najeriya cikin makon da ya gabata (6 ga watan Maris zuwa 12 ga watan Maris), kamar yadda Premium Times ta tattaro.

Rasa rayukan da aka samu a makon da ya gabata ya nuna alamun samun karuwar kashe mutane da kashi 900% idan aka kwatanta da na makon da ya shuÉ—e kafin shi.

Haka nan kuma alƙaluman mutanen da suka rasa rayukan su a wancan makon na baya shi ne ma fi ƙaranci tun bayan shigowar shekarar 2022.

Daga cikin mutum 103 da aka kashe, 24 jami'an tsaro ne da suka haÉ—a da sojoji 18, da yan sanda shida, yayin da sauran 76 duk fararen hula ne da basu ji ba kuma ba su gani ba.

Mafi yawan kashe-kashen sun auku ne a jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya, yayin da kalilan aka samu a wasu tsirarun jihohi.

Ba'a samu rahoton matsala a jihohin Zamfara, Sokoto da Neja ba, waÉ—an da babu tantamar cewa suna daga cikin jihohin da lamarin rashin tsaro ya fi wa illa.

Jaridar Premium Times ta tattara waÉ—an nan alkaluman ne daga labaran da kafafen watsa labarai suka ruwaito, babu adadin wanda ba'a rahoto ba.

Ga jerin yadda lamarin ya auku daki-daki:

Yan bindiga sun halaka mutum biyu kuma suka yi awon gaba da malamin Cocin Katolika, Joseph Akeke, a ƙauyen Kidendan dake jihar Kaduna.

Rahoto ya nuna cewa lamarin ya auku da ƙarfe 1:00 na daren ranar Talata lokacin da yan bindigan suka farmaki ƙauyen.

Mutum 82 a jihar Kebbi

Aƙalla Yan Bijilanti 63 aka tabbatar Allah ya musu rasuwa yayin da yan bindiga suka musu kwantan ɓauna ranar Lahadi da yamma.

Sarakunan yankuna biyu da lamarin ya shafa sun shaida wa BBC Hausa cewa Yan Bijilantin sun faÉ—a tarkon yan bindiga ne yayin da suka bibiyi yan ta'addan da suka hana yankunan zaman lafiya.

Sai dai wasu majiyoyi biyu na sarakuna sun tabbatar wa manema labarai cewa adadin yan bijilanti da aka kashe ya zarce 63.

Kwana biyu bayan haka, yan ta'adda suka halaka sojoji 18 da yan sanda 6 yayin da suka farmaki tawagar mataimakin gwamnan Kebbi, Sama'ila Yombe, a kauyen Kanya, ƙaramar hukumar Dangu Wasagu a jihar.

Lamarin ya faru ne lokacin da mataimakin gwamnan ya kai ziyarar jaje ga yankunan da ayyukan ta'addancin yan bindiga ya shafa.

Mutum 12 a Katsina

Ƙananan yara Bakwai suka rasa rayukan su yayin turereniyar mutane domin tserewa daga harin yan bindiga a Shimfida, karamar hukumar Jibia.

Lamarin ya faru ranar Alhamis da safe, awanni kaÉ—an bayan Sojojin dake aikin tsaro a yankin sun fice, a cewar mazauna ShinfiÉ—a.

Haka nan kuma, Fasinjoji biyar suka mutu wasu uku suka samu raunuka yayin da yan bindiga suka buÉ—e wa motoci wuta a hanyar Yan Tumaki – Danmusa.

Mutum É—aya a Ogun

Wasu makasa da ba'a san ko su waye ba sun banka wa Basaraken Olowe Gbagura, wuta a ƙaramar hukumar Abeokuta ta arewa, Akin Muheedeen.

Rahotanni sun nuna cewa Basaraken ƙauyen na kan hanyar dawowarsa daga masallaci sallar Asuba ne ya gamu da makasan da suka cinna masa wuta.

Wasu tsagerun yan bindiga sun tare hadimin gwamnan Taraba , Honorabul Gbashi, sun bindige shi har Lahira.

Wani wanda ke tare da mamacin ya bayyana cewa sun baro wurin Jana'izar da suka halarta yayin da maharan suka tare su.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN