Wata babbar Kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta tasa keyar Abba Kyari da wasu abokan harkallarsa su shida zuwa magarkamar NDLEA har zuwa ranar 14 ga watan Maris 2022.
Biyo bayan gurfanar da Kyari da abokan harkallarsa, da cacan kaki na shari'a da ya gudana tsakanin Lauyoyin Kyari da na hukumar NDLEA a cikin Kotu, Alkalin kotun Justice Emeka Nwite ya umarci a kai Kyari tare da abokan harkallarsa zuwa magarkamar NDLEA har zuw ranar 14 ga watan Maris.
Abokan harkallar Kyari da suka gurfana a Kotu sun hada da Mataimakin Kwamishinan yansanda ACP Sunday Ubua, Mataimakin Superintendent na yansanda ASP Bawa James, Inspector Simon Agirigba, Inspector John Nuhu, Chibuinna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.
Rubuta ra ayin ka