Hotuna da bidiyon ranar bakin ciki ga Kyari yayin da ya bayyana a gaban kotu


Dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriya kuma shugaban rundunar binciken sirri, DCP Abba Kyari, ya gurfana a gaban babban kotun tarayya dake Abuja a ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Kyari ya bayyana a gaban kotun tare da wasu 'yan sandan rundunar IRT da aka kama da zargin safarar hodar Iblis.

A karar mai lamba FHC/ABJ/57/2022, an zarge su da hada kai wurin aikata laifi, kangewa da kuma harkar safarar hodar Iblis da ta kai nauyin 17.55Kg.

A bidiyon da jaridar The Nation kuwa ta wallafa a shafinta na Twitter, an ga dakataccen babban dan sandan yana sunkuyar da kai yayin da ake kokarin nadar bidiyon.

Ya bayyana a kotun ne sanye da kaftani mai kalar duhu kuma ya sakaya fuskarsa da takunkumin fuska.

Ga bidiyon ku kashe kwarkwatar idon ku:

The Nation ta kawo rahoto a safiyar Litinin, 7 ga watan Maris 2022 cewa DCP Abba Kyari sun shigo kotu, ana sauraron a gurfanar da su a gaban Alkali. Jami’an hukumar NDLEA mai yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ne suka kai Kyari da ragowar ‘yan sanda da mutane biyu da ake zargi zuwa kotu.

Dakarun NDLEA biyu da suka jagoranci wadannan mutane da ake tuhuma, su na dauke da makamai.

Jaridar ta ce an ga Abba Kyari sanye da tufafi mai launin tsanwa a harabar kotun. Jami’in ‘dan sandan ya hallara ne a cikin wata katuwar motar gwamnati.

Ragowar mutane hudun da za ayi shari’a da su a zaman yau sun iso ne a cikin wasu motocin Hilux. A halin yanzu duk su na jiran zuwan malaman shari’a.

Legit


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN