An ceto dan ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Ali Isa Pantami, da aka rahoto cewa an sace shi a jihar Bauchi, Daily Trust ta rahoto.
A cewar majiyoyi, an gano dan ministan ne a Dambam, daya daga cikin kananan hukumomin jihar Bauchi a ranar Juma'a a shigen jami'an tsaro.
Majiyar ba ta bayyana ko an biya kudin fansa ba.
Al'amin Isa Ali Pantami yana zaune ne tare kakansa
Daily Trust ta tattaro cewa, wanda aka sace din, mai suna Al'amin Isa Ali Pantami, yana zaune ne tare da kakansa.
Da ya ke tabbatar da sako shi, daya daga cikin masu kula da shi ya ce:
"Yanzu muka baro gida; yana gida a yanzu. An gano shi a Dambam, inda wadanda suka sace shi suka ajiye shi. Sun sauke shi a wani shinge daga nan aka kawo shi gida."
Da aka tuntube shi a ranar Juma'a, babban limamin masallacin Isa Ali Pantami, Imam Hussaini, wanda da farko ya ki cewa komai game da lamarin, ya shaida wa Daily Trust cewa "Yaron yana gida."
Rundunar yan sandan Jhar Bauchi ta ce ba a kai mata korafi game da sace Al'amin ba
Amma, kakakin yan sandan jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ba a kai musu korafi kan lamarin ba.
Wakilin Daily Trust ya nemi ji ta bakinsa game da garkuwar.
"Abin da muke so daga mutane shine su taimaka mana da bayanai masu amfani kan mutanen da ba a yarda da su ba domin mu dauki mataki, kuma idan akwai wata matsala, a kai wa yan sanda rahoto."
Batun garkuwa da mutane ya yi wa al'umma katutu, an sha kira ga gwamnati ta dauki matakan kawo karshen matsalar.
Legit