Bayanan da ke fitowa daga fagen siyasar jihar Kebbi na cewa bisa ga dukkan alamu an kusa gane bakin zaren rikicin siyasar jihar Kebbi, kuma nan ba da dadewa ba wannan zaren da allura zai dinke barakar.
Yanzu kam bayyanar wasu hutuna, sun kara amintar da wannan hasashe a zukatan jama'a a fagen siyasar jihar Kebbi.
An gan Ministan sharia'a Abubakar Malami SAN tare da Sanata Adamu Aliero a wani ziyara da Sanata ya kai wa Minista a Abuja. Lamari da ya isa ya aike babbar sako ga magoya bayan tsagin guda biyu a fagen siyasar jihar Kebbi.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI