Dan Majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza Muhammad Bello Yakubu (Rilisco) ya fice daga jam'iyar APC ya koma jam'iyar PDP a jihar Kebbi.
Wani hadimin Dan Majalisar ya tabbatar wa shafin Jaridar isyaku.com cewa ta tabbata cewa Rilisco ya fice daga jam'iyar APC kuma har ya sayi Form na takara a karkashin jam'iyar PDP mai adawa a jihar Kebbi.
Sai dai kawo yanzu majiyar bata fayyace mana ko dan Majalisar ya fice tare da magoya bayansa bane ko yana shirin jawo su nan gaba...
Ku biuo mu don karin bayani....