Type Here to Get Search Results !

Umar Namashaya Diggi ya fadi matsayin Adamu Aliero kan rade-radin canja sheka daga jam'iyar siyasa a jihar Kebbi


Sakataren jam'iyar APC tsagin Adamu Aliero a jihar Kebbi Umar Namashaya Diggi ya ce tsohon Gwamnan kuma uban tafiyar tasu yana nan a cikin jam'iyar APC har yanzu a jihar Kebbi. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Umar Namashaya ya fitar da sanarwar haka a wani faifen bidiyo da ke yawatawa a shafukan sada zumunta na Facebook da dare ranar Alhamis .

Sai dai Namashaya ya ce inda maigidansu kuma jagoransu ya tafi nan zasu tafi, kenan idan ya koma wata jam'iya su ma za su koma jam'iyar da ya shiga. Ya ce amma a halin yanzu suna nan a jam'iyar APC.

Wasu yan siyasa a jihar Kebbi Ylyan jam'iyar APC, sun fice daga jam'iyar zuwa jam'iyar adawa ta PDP , cikin su har da Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunzu Muhammed Bello Yakubu wanda aka fi sani da suna Rilisco.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies