Yadda wasu barayi guda 5 suka tsere daga ofishin yansanda, duba abin da ya faru


Ranar Lahadi 27 ga watan Mayu wasu mutum biyar da ake zargi da laifin aikata sata sun tsrere daga ofishin yan sanda na Awak da ke karamar hukumar Kaltingo a jihar Gombe.

Kakakin hukumar yansandan jihar Gombe Mahid Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin a wata takarda da ya fitar amadadin Kwamishinan yansanda jihar ranar 30 ga watan Maris.

Sai dai ya ce bayan samun Labarin tserewar masu laifin ne, Yan sanda sun bazu inda tare da taimakon Yan banga suka sake kama uku daga cikin masu laifin da suka tsre.

Tun farko dai jama'a tare da Yan Banga suka kama mutum biyar bisa zargin fashe shago da aikata sata, kuma suka mika su ga ofishin yansanda da ke Awak. 

Wadanda aka sake kamawa sun hada da Bello Ibrahim mai shekara 19, Manasa Isaac shekara 18, Sani Bello shekara 18, yayin da har yanzu ba a kama Muhammed Yahaya da Bello Babawuro ba.

An shilla sashen SCID na Shelkwatar yansanda jihar da wadanda aka kama domin gudanar da kwakkwarar bincike yayin da ake ci gaba da neman wadanda ba a kama ba kawo yanzu.

Kazalika an fara gudanar da shari'ar cikin gida domin ladabtar da yansandan da suka yi sakaci har masu laifin suka tsere.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN