Type Here to Get Search Results !

Yansandan jihar Kebbi sun yi biris da zancen yajin aiki, Kwamishinan ya aike muhimmin sako


Jami'an yansandan rundunar yansandan jihar Kebbi sun yi biris da rade radin da ke zagayawa a shafukan labarai cewa yansanda za su gudanar da yajin aiki. Jaridar isyaku.com ya samo.

Jami'an sun bayyana wannan kudiri ne yayin wata tattaunawa na cikin gida tsakanin jami'an da Kwamishinan yansandan jihar Kebbi CP Musa Baba a shelkwatar yansandan jihar da ke birnin Kebbi.

Kwamishinan CP Musa Baba, ya bukaci jami'an yansanda na dukkannin mataki na girma su yi biris da zancen rade radin yajin aiki. Ya ce wasu masu gurbataccen manufa ne ke yada ire-iren wadannan labari. 

Ya kuma tuna wa jami'an yansanda cewa aikin dansanda na da kai'dodi, kuma yin yajin aiki daidai yake da yi wa tsarin aikin tarzoma.

Ya tabbatar wa yansandan jihar Kebbi cewa rundunar za ta inganta yanayin aiki da jindadin jami'anta a fadin Najeriya. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies