Type Here to Get Search Results !

Ko da gaske ne yan soshiyal midiya cike da jirgin sama sun tashi daga jihar Kebbi zuwa Abuja don taron APC na kasa?


Wata majiya mai tushe ta musanta zargin da ke yawatawa a jihar Kebbi cewa jirgin sama guda dauke da Yan soshiyal midiya ya tashi daga jihar Kebbi zuwa Birnin Abuja domin halartar taron jam'iyar APC na kasa da ake shirin gudanarwa. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Biyo bayan wani binciken gaggawa da shafin labarai na isyaku.com ya gudanar bayan zancen ya mamaye wasu manyan biranen jihar Kebbi a asirce, kuma cikin dan lokaci kalilan. An gano cewa ba haka zancen yake ba.

Mun binciko cewa zancen ya yi nassarar tasiri a asirce sakamakon kauce wa shafukan sada zumunta da aka yi wajen yada shi daga mutum zuwa mutum ta hanyar kira da wayoyin salula.

Wata majiya ta tabbatar mana cewa Yan soshiyal midiya hudu ne suka biyo jirgi zuwa Abuja, kuma sun biya wa kansu kudin jirgin ne. Yayin da saura suka biyo hanyar mota domin halartar taron.

Mu samo cewa, akwai zargin cewa an gan wasu yan siyasa tsagin Sanata Adamu Aliero a wani jirgin sama da ya tashi daga jihar Kebbi zuwa Abuja, kuma ana kyautata zaton cewa za su halarci taron kasa na jam'iyar APC ne. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies