An tsinci gawar Jaruma Takor Veronica a cikin wani daki na Otel a Jihar Benue, kamar yadda The Nation ta rahoto.
A cewar rahotanni daban-daban, an gano gawar na Veronica ne kimanin sati baya bayan ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta.
An rahoto cewa an tsinci gawarta ne a wani dakin otel a unguwar Nyinma na Makurdi. Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene ta tabbatar da afkuwar lamarin.
An kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisar jarumar, Anene Kakakin yan sandan ta ce an kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a mutuwar jarumar.
"An kawo rahoton mutuwar wata mata a otel amma muna jiran bayani daga likitoci. Ba mu ga alamun rauni a jikinta ba. Don haka gwajin likitoci zai sanar da mu sanadin mutuwarta. Matar da ta mutu tana sanye da tufafi; ba mu ga alamar rauni a jikinta ba.
"An kama mutane uku da ake zargi da hannu a wannan, za su bamu karin bayani. Ba za mu iya cewa kashe ta aka yi ba domin ba mu ga alamar rauni ba," in ji ta.
Abokanta da abokan aiki sun yi ta wallafa sakon ta'aziyya a dandalin sada zumunta.
Legit