Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: Yansandan jihar Kebbi sun bijire jita-jitan yajin aiki sun fito sun ...


Jami'an yansandan jihar Kebbi sun fito wajen aiki a duk wurare da yansanda ke gudanar da aiki a fadin jihar Kebbi, shafin Jaridar isyaku.com ya tattaro ranar Asabar 26 ga watan Maris 2022.

A wani zagaye da wakilinmu ya gudanar a garin Birnin kebbi ranar Asabar, mun samo cewa yansanda a ofishin Gwamnati na Cabinet office da ke birnin kebbi wanda suka hada da yansandan sashen SPU, Traffic warden da sauran sassa duk suna gudanar da aikinsu kamar yadda aka saba.

Kazalika wakinmu ya samo cewa babban ofishin yansanda shiyar Birnin kebbi, yansanda suna gudanar da ayyukansu. Rahoto ya ce hatta shelkwatar yansandan jihar Kebbi yansanda na ci gaba da gudanar da aikinsu.

A baya dai, wasu bata gari sun yada jita-jita cewa yansandan jihar Kebbi za su je yajin aiki ranar Asabar 26 ga watan Maris. Lamari da bai yi tasiri ba, domin dai yansandan jihar Kebbi sun bijire wa wannan jjta-jita kuma sun fito sun ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda aka saba. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies