Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC


Jam’iyyar APC mai mulki za ta gudanar da babban taronta na kasa a yau Asabar a Abuja.

Za a zabi sabbin shugabannin jam’iyyar na kasa da na shiyya a babban taron da za a gabatar a ranar 26 ga watan Fabrairu amma aka mayar ranar 26 ga Maris.

Ana sa ran taron zai amince da sassan kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka yi wa kwaskwarima da kuma amincewa da ayyukan kwamitin tsare-tsare na riko da na musamman (CECPC).

Wakilai 7,584 daga jihohi 36 na kasa da babban birnin tarayya Abuja ake sa ran za su halarci taron, shafin jamiyyar na Twitter ya tabbatar.

Wakilan za su zabi mambobi 22 na kwamitin ayyuka na kasa (NWC) daga cikin masu neman mukamai daban-daban 169 da za su karbi ragamar shugabancin jam’iyyar daga CECPC.

Babban abin jan hankali a taron na yau shine zaben sabon shugaba. ‘Yan jam’iyyar bakwai ne suka sayi fom din nuna sha’awa da tsayawa takara domin neman wannan mukami, wadanda suka fito daga yanki na tsakiya zuwa Arewa ta tsakiya.

‘Yan takarar sun hada da tsofaffin gwamnonin jihar Nasarawa biyu da sanatoci masu ci, Abdullahi Adamu da Tanko Al-Makura.

Al-Makura Ya Janye Daga Takarar Shugabancin APC, Ya Goyi Bayan Adamu

Al-Makura ya janye daga takarar shugabancin APC, ya goyi bayan Adamu a matsayin dan takarar yarjejeniya

Dan takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura ya janye daga takarar, kamar yadda kakakinsa, Danjuma Joseph ya tabbatar.

Sanata Al-Makura, tsohon gwamnan jihar Nasarawa wanda a halin yanzu yake wakiltar Nasarawa ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da wannan ‘yan sa’o’i kadan kafin taron da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 26 ga Maris, 2022 a Abuja. Ya yi alkawarin marawa Sanata Abdullahi Adamu baya

Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN