Matashin mai suna, Naziru Magaji, dan shekara 25 da ke kauyen Kununu Yalwa Danziyal, karamar hukumar Rimin Gado ta Jihar Kano ya tura wata tsohuwa, Habiba Abubakar, mai shekaru 80 cikin wata rijiya mai zurfi.
Naziru ya ce ya sha kwaya ne kuma cikin buguwarta ne ya je ya aikata wannan danyen aiki.