Yan ta'adda sun kai har ƙauyen Agunu Dutse, dake ƙaramar hukumar Kachia jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da mutum 47 kuma suka jikka wani ɗaya.
Wani mazaunin ƙauyen, Philp John, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch ya ce yan ta'addan sun shiga da daren ranar Ahamis misalin ƙarfe 1:00.
A cewarsa, ya bindigan sun zo da ɗumbin yawa kuma a ƙafa, suka rabu zuwa wurare Bakwai kuam suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin tsorata mutane.
Ya kuma yi bayanin cewa ƙauyen da lamarin ya faru na da nisan kilomita biyu kacan daga Barikin sojojin Akada.
John ya ce:
"Waɗan da suka sace sun haɗa da maza 16, ƙananan yara Tara da kuma mata 32. Mutanen garin ba zasu iya hana maharan ba saboda muggan makaman dake tattare da su."
"Har yanzun masu garkuwan da suka aikata haƙa ba su tuntubi kowa ba bare jin halin da mutanen ke ciki."
Shin jami'an tsaro suna da rahoton abin da ya faru?
Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, Mohammed Jalige, bai ɗaga kiran wayar da aka masa ba, kazalika bai turo amsoshin sakon da aka tura masa ba.
Haka na. har yanzu da muka tattara wannan rahoton, hukumomi a jihar Kaduna ba du ce uffan ba game da sabon harin da yan ta'dda suka kai.
Source: Legit.ng