Type Here to Get Search Results !

Buhari ya bawa yan Najeriya hakuri kan matsalar man fetur da wutar lantarki, duba abin da ya ce


Shugaba Muhammadu Buhari ya bawa yan Najeriya hakuri bisa daukewar wutar lantarki a kasa baki daya da kuma karancin man fetur da ya jefa yan kasar cikin wahalhalu masu yawa, rahoton Vanguard.

Shugaban kasar cikin wata sanarwa da hadiminsa Garba Shehu ya fitar ya nuna rashin jin dadinsa bisa mawuyacin halin da yan Najeriya suka shiga ciki sakamakon matsalolin.

A cewar shugaban kasar, 'gwamnati ta san cewa karancin man fetur din ya jefa yan kasa cikin mawuyacin hali kuma ya shafi kasuwancinsu, amma sauki na nan tafe.

Ina neman afuwar dukkan al'ummar kasa saboda wannan. Gwamnati na aiki dare da rana don magance matsalar. An aiwatar da tsari don magance karancin man fetur. Muna aiki tare da kungiyar manyan dillalan man fetur, MOMAN, da kungiyar dillalan fetur masu zaman kansu, IPMAN, kuma haka ya fara cimma ruwa.

"An samu isashen man fetur a wasu jihohi, duk da layi a gidajen mai. A cikin yan kwanakin nan, muna sa ran sauran jihohin su samu man.

"An tanadi kudi domin tabbatar da mai a kasar don gaba. Farashin makamashi ya tashi a kasuwan duniya a baya-bayan nan, amma gwamnati za ta tabbatar hakan bai shafi yan Najeriya ba."

Legit

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies