Da duminsa: Soji sun halaka fiye da yan bindiga 100 da ke addabar kudancin jihar Kebbi da Niger (Bidiyo)


Rahotanni da duminsu na cewa jami'an tsaro sun halaka yan bindiga fiye da 100 a tagwayen ayyukan kakkaban yan bindiga da suka addabi yankunan jihar Niger da kudancin jihar Kebbi. Jaridar isyaku.com ya samo.

Mun samo cewa jami'an tsaron soji da Yan sa Kai sun yi wa yan bindigan kisan Allah tsine a yankin garuruwan Shambo, warari, da kuma Bangi da ke karamar hukumar Bariga a jihar Niger ranar Laraba 16 ga watan Maris.

Wata majiya ta labarta cewa ana kyautata zaton cewa yan bindiga da suka farmaki garin Nasko tare da kashe DPO da yansanda 7 na daga cikin wadanda suka halaka a wannan farmaki.

Latsa kasa ka kalli bidiyo

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=4988325167922638&id=100002356131261

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN