Yan bindiga da dama sun mutu yayin da jirgin yaƙin rundunar sojin sama ya saki bama-bamai a shagalin auren dan bindiga



Yan bindiga da dama sun mutu yayin da jirgin yaƙin rundunar sojin sama (NAF) ya saki ruwan bama-bamai a shagalin aure da aka shirya wa ɗaya daga cikin shugabannin yan bindiga a Katsina.

Leadership ta rahoto cewa daga cikin waɗan harin ya tura barzahu har da wani mai suna Sule, wani sanannen jagoran yan bindiga, ɗan uwan makashi, Lalbi Ginshima.

Dakarun sojojin sun kaddamar da wannan farmakin ne a ƙauyen Unguwar Adam, ƙaramar hukumar Dan Musa a jihar Katsina.

Wata Majiyar fasaha ta bayyana cewa dakarun sojin sun samu rahoton sirri na cewa an ga yan bindiga sun nufi Anguwar Adam daga kauyen Ɗan Alikima domin ɗaura auren ɗaya ɗaga cikin shugabannin su.

Wani babban jami'in fasaha a rundunar soji ya shaida wa PRNigeria cewa:

"Bisa wannan bayanai, Sojojin sama suka tashi jirgin sama domin sa ido kan lamarin a a yankin da kuma tabbatarwa."

"Bayan wani ɗan lokaci jirgin ya tabbatar da sahihancin labarin saboda ganin yan bindiga sama da 50 na shagalinsu a wurin."

A cewar jami'in, Jirgin ya cigaba da bibiyar lamarin kuma ya tura wa jirgin yaƙi adireshin wurin da yan ta'addan suka koma a arewacin Anguwar Adam.

Ya ce:

"Jirgin yaƙin na isa wurin ya gano akwai sama da yan bindiga 50, va da ɓata lokaci ba ya fara harba musu rokoki, igwa da sauran makamai."

Shin mutanen yankin sun san abin da ya auku?

Wata majiya a ƙauyen ta bayyana cewa yan ta'addan sun yi babban rashi, domin dabyawan su sun bakunci lahira, wasu da dama sun ji munanan raunuka.

"An yi wa yan ta'addam mummunar ɓarna, aƙalla 27 daga cikin su sun tafi gana wa da Allah, yayin da wasu da yawa suka ji muggan raunuka."

"Daga cikin waɗan da aka sheke har da shugaban yan bindiga Sule, ɗan uwa ga ƙasurgumin ɗan bindiga, Lalbi Ginshima."

Wasu tsagerun yan bindiga sun tare hadimin gwamnan Taraba , Honorabul Gbashi, sun bindige shi har Lahira.

Wani wanda ke tare da mamacin ya bayyana cewa sun baro wurin Jana'izar da suka halarta yayin da maharan suka tare su.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN