Matashiyar budurwa ta halaka tsohon saurayinta kan kyautar N3,000 da zasu raba


Rundunar yan sanda reshen jihar Legas ta damƙe wata budurwa yar shekara 26, Oluwatoyin Joshua, bisa zargin sheƙe tsohon saurayinta.

Tribune Online ta rahoto cewa ana zargin matashiyar ta sheke saurayin ne kan kyautar N3,000 a yankin Shangisa dake cikin Legas.

Jami'i mai zana hotuna na hukumar, Adekunle Ajisebutu, a madadin kwamishinan yan sanda, ya ce wani mai kyayyawan niyya ne ya ba su kyautar kudin.

Budurwar, wacce ta shiga dana sani kan abin da ta aikata tace ta halaka tsohon saurayin nata ne a kokarin kare kanta.

A jawabinta ta ce:

"A ranar na je ganin tsohon saurayina Adebayo a wurin da yake siyar da muggan kwayoyi, ina wurin wani abokinsa, É—an danfarar Intanet ya zo ya bani kyautar N3,000, lokacin ya na shirin yin tafiya."

"Ya umarci na É—auki dubu É—aya na bai wa tsohon saurayi na N2,000, daga na ya yi tafiyarsa. Saboda haka naje wurin Adebayo domin na sanar masa yadda muka yi da abokinsa."

"Nan fa ya ce ƙarya nake yi baki ɗaya kuɗin nasa ne. Na faɗa masa bai isa ya kwace kuɗin duka ba, na aje masa N2,000 a kan Tebur na kama gabana."

Meya jawo har akai kisan?

A cewar matashiyar budurwan, nan take sai ya watsa mata kudin a fuska, ya É—auki waya ya kira mutumin da ya ba su kudin.

Ta cigaba da cewa:

"Kafin na ankara ya fara jibgata, na kai kararsa wurin dattijon Anguwa, ya gargaÉ—e shi ya kuma umarce shi ya bar wurin baki É—aya."

"Bayan an fitar da shi da tsiya sai ya sake dawo wa ya cigaba da narka ta, garin haka ne na shiga ɗakin girki na sunkuto wuƙa domin na tsorata shi."

"Ina kokarin guduwa daga wurinsa ne ya sa wani fasasshen tayil ya dake ne a ka, ni kuma na yanke shi a wuya, nan da nan aka kai shi Asibiti, bayan awa uku ya ce ga garinku nan. Ni na biya kudin kai shi Asibiti."

Tsagwaron kishin mata ya yi sanadin rasuwar wani Mai mata biyu yayin da yake yi wa Uwar gida bankwana zai koma dakin Amarya.

Rahoto ya nuna cewa Uwar gidan mai suna Atika ta daba wa mijinsu wuka har lahira a Mararaba dake jihar Nasarawa.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN