Yadda dan shekara 17 ya taushe Almajiri mai shekara 12 ya kwakwale idonsa na dama da karfin tsiya, duba dalili (Hotuna)

Isah Hassan wanda ya kwakwale idon Almajiri

Rundunar yansandan jihar Kano ta kama wani saurayi mai suna Isah Hassan dan shekara 17 bisa zargin kwakwale idanun wani Almajiri a jihar Kano ranar 20 ga watan Maris. Shafin Jaridar isyaku.com ya ruwaito.

Wata sanarwa da Kakakin hukumar yansandan jihar Kano ya fitar na cewa wanda aka kama ya dauki wani Almajirai dan shekara 12 mai suna Mustapha Yunusa daga rukunin gidaje na Sheka Dantsinke Quarters, a karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, ya kai shi rukunin gidaje na Rimin Hamza,a karamar hukumar Tarauni a jihar Kano ya daure hannayen Almajirin ya yi amfani da wuka mai tsini ya kwakwale idonsa na dama da karfin tsiya.

Sanarwar ta kara da cewa yansanda sun kama wanda ake zargin kuma ya gaya masu cewa ya kwakwale idon Almajirin ne domin wata tsohuwa mai shekara 100 mai suna Furera Abubakar wacce suke zaune a unguwa daya, ta ce ya kawo mata idon dan Adam domin ta yi masa asirin bacewa ko baduhu.

Mustapha Yunusa Almajirin da aka kwakwale wa idon dama

Sakamakon haka ya aikata wannan danyen aiki wa Almajiri. Ya ce bayan ya kwakwale idon kuma ya kai mata, sai ta bukaci ya bayar da naira 500 wanda baya da su a lokacin. Sakamakon haka sai ya je ya boye idon.

Sai dai bayan kwana uku, ya kula cewa idon ya ruba yana wari, sai ya je ya yar da idon. Binciken yansanda ya kai ga kama shi daga karshe, tare da tsohuwa yar shekara 100 da ta bukaci ya kawo mata idon dan Adam domin ta yi masa asirin bacewa. 

Furera Abubakar tsohuwa mai shekara 100 da ta ce a kawo idon dan Adam ta yi asirin baduhu ko layar Zana

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN