Rundunar yansandan jihar Adamawa ta kama wani matashi dan shekara 31 mai suna Nicodemus Ignatius bisa zargin kashe mahaifinsa mai shekara 75.
Nicodemus ya kashe mahaifinsa ne a Unguwan Bistel da ke garin Song, a karamar hukumar Song ranar 3 ga watan Maris bayan ya dawo daga wajen kwankwadar barasa.
Rahotanni na cewa Nicodemus ya dawo gida da karfe 8:00 na dare ya tarar da mahaifinsa da mahaifiyarsa a cikin daki, sai ya kulle dakin daga waje.
Bayan mahaifinsa ya farga da abinda dansa ke kokarin yi na kone gidan yayin da suke ciki da mahaifiyarsa, sai mahaifin ya ketare taga ya fito. Sai dai fitowarsa ta taga ke da wuya sai dansa Nicodemus ya yi amfani da wani itace da yake rike a hannunsa ya kai wa mahaifinsa duka har ya same shi a kai kuma kansa ya tsage sakamakon haka tsoho ya mutu.
Kakakin hukumar yansandan jihar Adamawa DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin.
Nicodemus ya yi nadamar kashe mahaifinsa. Ya ce ya zuki tabar wiwi ne fiye da kima a ranar da ya kashe mahaifinsa.
Rubuta ra ayin ka