Ta tabbata jihar Kebbi ta shiga sahun jihohi da suke fuskantar tabarbarewar tsaro sakamakon aukuwar kashe-kashe da ayyukan Yan bindiga ya haddasa, musamman a kudancin jihar Kebbi.
Masarautun Zuru da Yauri sun zama fagen gwajin dafi na ayyukan Yan ta'adda inda suke amfani da duhun dajin wannan yanki suna gudanar da ayyukansu.
Wane tanadi Gwamnatin jihar Kebbi ta yi kan harkokin tsaro?
Samun cikakken bayanan tsaro da ya shafi tsare-tsaren dubarun tafiyar da harkar tsaro yana da matukar wuya, domin mahukunta basa bayyana tsarinsu a faifai saboda dalilan tsaro.
Sai dai ana gani a kasa cewa Yan ta'adda ke yawan kai wa jama'a har da jami'an tsaro farmaki har kuma su kashe su.
Wasu masana suna ganin cewa lokaci ya yi da jami'an tsaron jihar Kebbi za su fara kai wa Yan ta'addan farmaki a mabuyarsu tun kafin su hadu su kai wa jami'an tsaro da jama'a farmaki a garuruwansu.
Ko Gwamnatin jihar Kebbi tana tuntubar tsoffin jami'an tsaro a jihar?
Wani bincike da Jaridar isyaku.com ya gudanar, ya nuna cewa har yanzu babu wani bayyanannen tsari ko shiri daga bangaren Gwamnatin jihar Kebbi wajen tuntubar tsoffin jami'an tsaro a jihar ka kan neman mafita game da kalubalen tsaro a fadin jihar Kebbi. Ko da akwai, bamu sani ba kuma ba a wadatar da bayani a kafofin labarai na jihar Kebbi ba dangane da wannan zance.
Akwai Janar na soji da dama, AIG na yansanda da sauran jami'an tsaro da na DSS a jihar Kebbi masu murabus.
Duk da irin tarin wadannan hafsoshin tare da sauran mukamai na hukumomi da suka yi wa aiki har suka yi ritaya. Jihar Kebbi kawo yanzu bata jawo su cikin harkar tsara dabarun tsaro ba bisa la'akari da kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.
Daga cikin tsoffin jami'an tsaro a jihar Kebbi akwai masu hazakar kimiyyar zamani
Kafin hukumar yansandan Najeriya ta fara amfani da na'urar binciken diddigin sirri (Tracker) a 2017, akwai wani tsohon jami'in tsaro na hukumar DSS da ya fara gudanar da wannan aiki a asirce saboda dalilan tsaro tun 2016 karkashin Seniora Technical Services (Seniora Tech) wanda ke karkashin Kamfanin Seniora Intl Ltd a kan titin Ahmadu Bello da ke garin Birnin kebbi.
Wannan kamfani ya samar da wadataccen ilimin tsaron wayoyin salula ga matasan jihar Kebbi tare da kasancewa Kamfanin farko na asalin dan jihar Kebbi da ya fara ganowa tare da mayar wa jama'a wayoyinsu na salula idan aka sace masu a waccan lokaci ta hanyar wannan kimiyya a tarihin jihar Kebbi.
Ababen da ya kamata Gwamnatin jihar Kebbi ta yi da gaggawa
1. Ta kira taron tsofaffin jami'an tsaro domin tattaunawa da Gwamnati da kuma takwarorinsu da ke aiki a yanzu kan samar da shawarwari domin samar da mafita ga kalubalen tsaro da jihar Kebbi ke fuskanta.
2. A saurari kwararrun tsofaffin jami'an tsaro da suka yi fice wajen wata harkar tsaro na zamani, aikace ko a hikimnce, su bayar da shawara domin samar wa jama'ar jihar Kebbi mafita kan kalubalen tsaro.
3. A gayyaci kwararru kan harkar tsaro masu zaman kansu domin yin kwangilarsu kan wasu harkokin tsaro da zai samar da damar yin aiki tare da jami'an tsaro na Gwamnati domin samun cikakken nassara kan harkar tsaro.
4. Gwamnatin jihar Kebbi ta sama wa jami'an tsaro kayakin zamani na damarar fuskantar Yan ta'adda a ko da yaushe.
5. Gwamnati ta dauki nauyin ilmantar da akalla yaro daya ko biyu daga yaran jami'an tsaro wadanda aka kashe wajen yi wa jihar Kebbi aiki har zuwa mataki na Digiri tare da sama masu aiki idan sun gama karatu.
6. Gwamnati ta samar da damar saka wa Yan sa Kai tare da Yan Banga da suka mutu wajen kare kasarsu da yi wa jama'a hidima sakamakon yin artabu da Yan ta'adda ta hanyar yi wa iyalansu wani ihsani mai kwari. Domin hakkin Gwamnati ne ta kare rayuwa da dukiyar al'ummarta.
7. A samar da sashe na musamman da za a wadatar da na'urorin tsaro na zamani a karkashin sashen tsaro na jihar Kebbi da zai zama dakin gudanar da harkokin tsaro, watau Security operation cordination situation control unit.
Ta wannan sashe za a dinga hada bayanai da tsare-tsaren da ake samarwa domin aiwatar da matakai da ake daukawa na bai daya wajen tafiyr da harkar tsaro a jihar Kebbi.
8. Gwamnati ta yi kwamgilar jaridu da, shafukan labarai masu zaman kansu da Bloggers wadanda ke da cikakken rijista kuma masu zaman kansu Yan asalin jihar Kebbi domin taimakawa kafafen watsa labai na Gwamnati a zamanance, da kuma samar da sahihan labarai na gaggawa ga al'ummar jihar Kebbi, domin kauce wa illolin labaran yara yan soshiyal mediya.
Ra'ayin Isyaku Garba Zuru