Garin Birnin kebbi babban Birnin jihar Kebbi ranar Asabar 11 ga watan Maris ya tashi cikin kura irinsa na farko a shekarar 2022.
Har zuwa tsakiyar rana karfe12:54 kura ya lullube Rana. Wasu ababen hawa sun kunna fitilar ababen hawa domin ankarar da sauran ababen hawa a kan titunan garin Birnin kebbi.
Rahotanni na cewa an shiga irin wannan yanayi a makwabtan jihohin Sokoto da Zamfara. Lamari da akan yi fama da irinsa na yan makonni a kowane shekara a yawancin jihohin arewa.