Wani abun ban dariya da mamaki ya auku bayan wasu guragu da suka dade suna bara sun tashi suka ruga da gudu bayan Jami'ai sun yi kokarin kamasu a garin Thika da ke kasar Kenya. Shafin Jaridar isyaku.com ya samo.
38 daga cikin guragu da aka yi kokarin kamawa sun gudu da kafafunsu, wasu har sun fi Jami'ai gudu, domin dai sun kasa kamuwa bayan sun bude da gudu domin kaucewa kamasu.
Hukumomi na kokarin tsabtace garin ne sakamakon yadda mabarata suka cika muhimman hanyoyi kuma suna damun mutane da barace-barace.
Wani abin mamaki shi ne yadda wata mata wacce take rarrafe a kasa tana bara lokaci mai tsawo, ta mike ta ruga da gudu babu ko waiwaye domin kauce ea kamata.
Rubuta ra ayin ka