Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: Mahaifiya ta watsa wa diyarta mai shekara 10 fetur ta banka mata wuta, duba dalil


Yansandan jihar Ogun sun kama wata matar aure mai yara biyar bayan ta zuba wa diyarta mai shekara 10 man fetur ta banka mata wuta ranar 20 ga watan Maris. Shafin Jaridar isyaku.com ya samo.

Rahotanni na cewa matar mai suna Aisha Tijani, ta zuba wa diyarta man fetur ta kunna mata wuta cikin tsananin bacin rai bayan yarinyar ta maida wa dan'uwanta wayar salula da mahaifiyarsa ta kwace.

Wani ganau, kuma makwabcin Aisha mai suna Moroof Ayinde ne ya kai kara wajen yansanda, bayan ya gan abin da ya faru.

Kakakin hukumar yansandan jihar Ogun ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce ana gudanar da bincike a sashen CID kuma za a gurfanar da Aisha a gaban Kotu da zarar sun kammala bincike.

An garzaya asibiti da yarinyar inda take samun kulawan Likitoci sakamakon kunar wuta da ta samu. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies