Type Here to Get Search Results !

Yadda ginin ban dakin makaranta ya kashe yara kanana guda biyu bayan ya rufta masu a jihar Niger


Yara biyu sun mutu bayan ban daki ya rufta masu a UK Bello Memorial Primary School da ke garin Paiko, a karamar hukumar Paikoro da ke jihar Niger.

Daily trust ta ruwaito cewa ba wanda ya san abin da yaran ke yi a gefen bangon ginin wanda tun asali yake da rauni kafin ruftawarsa kan yaran.

Wasu ganau sun ce yaran, yaro da yarinya, suna tallar piya wata ne, wasu kuma sun ce yaran suna tsintar ababe ne tare da sauran yara kafin ginin ya rufta masu, kuma suka mutu nan take.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies