Shugaban karamar hukuma ya lakaɗa wa Kansila dukan tsiya a bainar Jama'aHayaniya ta hautsine a karamar hukumar Ndokwa ta gabas yayin da ake zargin shugaban karamar hukumar, Mr Juan Governor, da lakada wa wani kansila, Louis Ogene bakin duka.

A ranar Asabar, The Punch ta tattaro bayanai akan yadda sauran kansiloli da ‘yan kallo suka yi gaggawar zuwa harabar ofishin karamar hukumar don ceto Ogene.

Yayin bayani akan artabun da suka yi, kansilan ya kada baki ya ce:

“Majalisar ta dade tana bukatar bayanai dangane da kudaden shiga da na fita na karamar hukumar, wanda daga nan aka bukaci ma’aji ya yi wa majalisa bayani.”

Tambayar takardun shige da ficen kudin ne ya hassala shugaban karamar hukumar

Ya ci gaba da cewa:

“Ma’ajin ya fara gabatar da bayanai ga majalisar ba tare da kawo wata takardar shaidar kudaden ba don kowa ya gani.

“Ganin haka ne wani abokin aikin mu ya bukaci a gabatar wa majalisa da takardar, amma sai shugaban karamar hukumar ya ce mu kyale ma’ajin ya kammala bayanin, daga bisani ya kawo takardun. Sai muka kyale don zaman lafiya.

“Bayan kammala bayanin, sai ma’ajin ya mika wa shugaban karamar hukumar takarda da ya gama karantawa. Shugaban karamar hukumar ya amshi takardar inda ya ce zai samar wa kowa takardar don mu ajiye a wurin mu. Har yau bai sake magana a kai ba duk da wannan maganar ta shafe makwanni da dama.

“Sai dai a zaman da muka yi makon da ya gabata, ranar Talata, 8 ga watan Maris na 2022, an kara daga maganar. A matsayina na shugaban harkokin shige da ficen kudi na karamar hukumar, na nemi ganin takardar, wanda daga nan ya dauke ni da mari.”

Ganin ‘yan daban Governor a wurin yasa ya kasa rama marin

Ya ci gaba da cewa bai iya ramawa ba saboda akwai yaran sa ‘yan daba ta ko ina.

Daga na ne shugaban kansiloli masu rinjaye da majalisar suka daga maganar har ta kai hakan a cewar sa.

Yayin da wakilin The Punch ya nemi jin ta bakin Governor, ya ce babu abinda zai iya cewa sannan ya kashe wayar.

Kansiloli 13 duk sun kalubalanci salon mulkin shugaban karamar hukumar, hakan yasa suka mika takardar korafi ga majalisar Jihar Delta don ta shiga cikin lamarin.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN