Yadda Bianca Ojukwu ta kaftawa matar tsohon gwamna mari (Bidiyo)


Charles Soludo, zababben gwamnan Jihar Anambra da aka rantsar a ranar Alhamis 17 ga watan Maris na 2022 ya nuna damuwarsa kan musayar maganganu da mari da aka yi tsakanin matar gwamna mai barin gado, Ebele Obiano da Bianca Ojukwu.

Da ya ke magana minutuna bayan afkuwar lamarin, Soludo, wanda ya mayar da hankali wurin rattaba hannu kan takardun rantsar da shi ya ce wadanda ke son barin wurin suna iya tafi, rahoton Vanguard.

Soludo ya rattaba hannu kan takardun ne a gaban babban alkalin Jihar Anambra, Mai Sharia Onochie Anyachebelu da wasu mazauna jihar da suka hallarci taron.

Sabon gwamnan da aka nada ya sanar da mutanen Anambra cewa jihar ta mayar da hankali ne wurin cigaba kuma jiha ce wacce ake bin doka da oda.

Yadda lamarin ya faru

Tuda farko, Wani abu mai kama da dirama ya faru a wurin kaddamar da Farfesa Charles Soludo a matsayin gwamnan jihar Anambra a yayin da matar gwamna mai barin gado, Willie Obiano, Ebelechukwu, ta mari Mrs Bianca Ojukwu a wurin taron, rahoton Daily Trust.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ta bakin wakilinta da ke wurin taron ta rahoto cewa lamarin ya faru ne nan take bayan Solodu ya yi rantsuwar kama aiki.

NAN ta rahoto cewa manyan baki ciki har da tsohon gwamna Obiano sun riga sun zauna yayin da Mrs Obiano ta shigo ta wuce layin gaba inda tsohuwar matar na Dim Odumegwu Ojukwu ke zaune ta sharara mata mari.

Hakan ya janyo hankalin jami'an tsaro da wasu mutane da suka kwato Mrs Obiano daga hannun Bianca wacce bisa ga alamu ta yi mamakin abin da ya faru.

Daga bisani an tafi da Mrs Obiano daga wurin taron, shi ma mijinta ya bar wurin taron bayan afkuwar lamarin da kuma rantsar da sabon gwamnan.

Latsa nan ka kalli bidiyon Marin

https://mobile.facebook.com/charles.ogbu2/videos/1550679191998534/


Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN