Kotu a jihar Kebbi ta ce bata da hurumin sauraron karar da wasu mambobin jam'iyar APC reshen jihar Kebbi suka shigar a gabanta watannin da suka gabata.
Alhaji Bala Sani Kangiwa ya sanar da haka a wani faifen bidiyo da ke yawatawa a shafukan sada zumunta wanda Yusha'u Nata'ala ya nada jim kadan bayan fitowa daga Kotun a garin Gwadangaji.
Jam'iyar APC reshen jihar Kebbi ta tsunduma cikin rikici da ya kai ga sauke wasu shugabanninta yan watanni da suka gabata. Sakamakon haka wadanda suke ganin ba a yi masu daidai ba suka garzaya Kotu.
Latsa kasa ka kalli cikakken bayanin abin da ya faru a Kotu.