Budurwa jaruma mafi tsawo a Duniya ta magantu kan yadda tsawonta ke shafar neman soyayyar rayuwarta, duba ka gani (Hotuna)


Wata budurwa Jarumar kasar Rasha mai tsawon kafa 6ft 9in ta ce ita kam tana fama da matsalar samun masoyi a rayuwarta saboda tsawonta. Jaridar isyaku.com ya samo.

Ekaterina Lisina, ita ce ke da lambar mace wacce ta fi kowace Jaruma tsawo a Duniya. Kuma ta taba kasancewa mai lambar Guinness World records na mace da ta fi kowace mace dogayen kafafu a Duniya.

Ta ce wannan lamari yana haifar mata da matsalar gaske wajen samun masoya a rayuwarta.

Ekaterina tsohuwar yar wasar kwallon kwando ce kafin ta zama Jaruma a halin yanzu a kasarta ta Rasha. 


Previous Post Next Post