Rundunar hukumar hana fasakwabri reshen jihar Kebbi ta yi nassarar kama wata babbar mota makare da naman jaki na miliyoyin nairori. Shafin labarai isyaku.com ya samo.
Ranar Asabar 5 ga watan Maris, jami'an rundunar na shiyar Birnin kebbi, sun kama motar Trela mai lamba ARG 323 XA makare da naman jaki wanda aka da a cikin buhuna.
Kakakin hukumar na reshen jihar Kebbi Nasiru Manga, ya sanar wa manema labarai a wata takarda da ya fitar amadadin Konturola na hukumar reshen jihar Kebbi. Ya ce duk da yake an biya kudin kaidar watau Duty na Naira miliyan 42,534,400.
Sai dai ya ce kasuwancin haramtacce ne bisa dokar kasa ta Section 63 (b) of CEMA CAP C.45 LFN 2004, wanda ya jibanci harkar naman jaki da saurar dokoki.
Daga karshe rundunar ta kone naman jakin, a gaban wakilan hukumomin DSS, NESREA, da kuma yansanda.