
Wata mata ta je ban daki domin yin lalura kwatsam sai ta haifi jariri ba tare da sanin tana dauke da juna biyu ba
March 23, 2022
Wata mahaifiya ta ce bata san tana dauke da juna biyu ba sai da ta je ban daki domin yin lalura sai ta kula ashe nakuda take yi kuma ta haihu da tsakiyar dare.
Nicola Thomas yar shekara 36, kuma.mahaifiyar Yara biyu tana zaune ne a Cardiff, da ke Wales, ta ce takan yi fama da murdawar Mara, lamari da take wa daukar sha'anin al'adarta ne duk tsawon lokacin da take dauke da juna biyun.
Sai dai ranar 15 ga watan Maris, kwatsam sai ta haihu cikin dare yayin da ta shiga ban daki domin yin lalura.