Wani yaro dan shekara 18 ya kashe wata matar aure ta hanyar kwada mata tabarya a kai har sau biyu saboda ya sami sukunin sace mata wayoyin salula guda biyu da ya gani a dakinta a jihar Kano.
A wani bidiyo da Kakakin hukumar yansandan jihar Kano ya fitar a shafinsa na sada zumunta, yaron ya ce ya shiga gidan ne ya tarar da matar tana barci, sai ya shiga dakin dafa abinci ya dauko tabarya ya je ya kwada mata a kai, daga bisani ya kwada wa yaranta guda biyu tabaryar a kai duk da ya tarar da su suna barci.
Ya ce daga bisani ya kwashe wayoyinta ya je ya sayar da su .Allah ya yi wa matar rasuwa cewar wata majiya. Sai dai majiyar ta ce yaran basu mutu ba amma suna cikin wani mawuyacin hali.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI