Yanzu yanzu: Rikici ya kaure a kungiyar Yan Jarida na kasa NUJ reshen jihar Kebbi, jigo ya bayyana wani sirri

Abubakar Attahiru Dakingari


Abubakar Attahiru Dakingari jigo a kungiyar Yan Jarida na kasa reshen jihar Kebbi ya magantu kan rikicin shugabanci da ya taso a kungiyar. Shafin Jaridar isyaku.com ya ruwaito.

Ya yi karin haske kan muhimman ababe da ya yi zargin cewa suna cikin shika-shikan kura-kurai da suka taru suka haifar da manyan matsaloli da suka taso a kungiyar.

Ya yi zargin cewa Mataimakin shugaban kungiyar da wasu suka ce sun rantsar a ranar Laraba a wani Kangon gini ba ma cikakken dan kungiyar Yan Jarida na kasa reshen jihar Kebbi bane.

Yunkurin mu na jin ta bakin Usman Abdullahi Shehu kan lamarin ya ci tura sakamakon wasu matsaloli da suka haifar da uzurra.

Latsa kasa ka kalli takaitaccen bayani


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN