Tsohon Gwamnan jihar Anambra sanye da gajeren wando a hannun EFCC, duba dalili (Bidiyo)


Wani faifen bidiyo da ke yawatawa a intanet ya nuna tsohon Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano sanye da gajeren wando a hannun hukumar EFCC. Shafin isyaku.com ya samo.

An gano Obiano yana shan ruwan gora a ofishin EFCC bayan jami'an hukumar sun kama shi ranar Alhamis 17 ga watan Maris bayan karewar wa'adinsa na mulkin jihar Anambra.

Wannan yana zuwa ne bayan EFCC ta ce ta kai tsohon Gwamnan ofishinta na Abuja bayan kama shi a birnin Lagos yayin da yake kokarin ficewa Najeriya zuwa kasar Amurka.

Latsa kasa ka kalli bidiyo

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=10221218776834097&id=1086336452

Previous Post Next Post