Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: An bindige shugaban Mata na jam'iyar APC har Lahira, duba yadda ta faru


An bindige shugaban Mata na jam'iyar APC na mazabar Koro a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara , Mrs Olomi Sunday har Lahira bayan Yan Banga sun yi kokarin ceto ta daga hannun masu garkuwa da mutane. Shafin Jaridar isyaku.com ya samo.

Mun samo cewa an riga an hada N20m da masu garkuwa da mutane suka bukata kafin su sako wadanda suka sace. Sai dai Yan Banga sun hana a bayar da kudin kuma suka yi kokarin ceto ta.

Mrs Olomi ta rasa ranta a gumurzu da aka yi tsakanin Yan Banga da masu sace mutanen. Wasu daga cikin Yan bangan sun sami raunuka bayan sun yi wa masu garkuwa mumunan lahani.

Mrs Olomi tana cikin shugabannin mazabu uku da aka sace a motar bas mai daukar mutum 18 lokacin da suke kan hanyar komawa gida bayan sun halarci taron kaddamar da shugabannin jam'iyar APC na jihar Kwara a babban Birnin jihar mako da ya gabata.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies