Duba matashiyar budurwa mai shekaru 14 dake sana'ar saka tayils


Fatima Saqibu Abubakar yarinya ce mai shekaru 14 a duniya mai zama a Ja’en kwatas a karamar Kumbotso ta jihar Kano.

Fatima tana aikin saka tayil a Kano, sana'a ce wacce aka san maza ke yin ta. Fatima ta sanarwa da Daily Trust cewa ta koyi aikin ne daga mahaifinta a shekaru kadan da suka gabata kuma tana zuwa makaranta.

Daily Trust ta bayyana cewa, a cewarta, ta fara karatun firamare a shekarar 2013 kuma yanzu haka tana aji hudu na sakandare.

"Shekaru kadan da suka gabata na fara aikin nan. Ina hango shi a matsayin mai matukar amfani gareni duk da ni mace ce. Ba zan yi zaman banza ko rashin aiki ba.

"A gaskiya an fi ganin aikin saka tayil a matsayin aikin maza. Toh idan mace za ta iya koyon shi kuma ta kware, za ta zama dalilin da zai sa wasu yara matan sun koyi sana'ar domin dogaro da kai," tace.

A hankali tace ta fara ce wa mahaifinta ya bata dama ta gwada. Ya sha mamaki amma kuma ya bata dama.

"Ya hada min siminti kuma cike da mamaki ya ga na fara aiki me kyau. Daga nan na fara aiki da balallun tayils kuma a gida. Makwabta sun fara sani kuma suka fara bani aiki," tace.

Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN