Rahoto daga jaridar Daily Trust ya ce, an kashe mutane hudu a yankin Obayantor da ke karamar hukumar Ikpoba Okha ta jihar Edo bayan wani rikici da ya barke tsakanin wasu matasa da jami’an sojojin Najeriya.
Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya yi zargin cewa wani ne ya dauki hayar sojoji ga al’umma da nufin kwato Okhaegele, kuma a lokacin fasinja an kashe sojoji biyu. Ya ce daga baya sojojin suka kaddamar da harin ramuwar gayya ga al’umma.
Wata majiya daga yankin ta ce sojojin sun zo da yawa inda suka rika harbe-harbe a sama, lamarin da ya tilastawa mutanen tserewa domin tsira da rayukansu. Ya ce an harbe mutane hudu har lahira.
Sai dai mai magana da yawun hedkwatar brigade 4 na rundunar sojin Najeriya, Benin, Yemi Sokoya, ya musanta cewa an yi hayan sojoji zuwa yankin.
Ya kuma yi watsi da labarin kashe sojoji biyu.
A cewarsa:
“Ba a yi hayan sojoji aiki ga al’ummar ba kuma ba a kashe wani soja ba. Ba harin ramuwar gayya ba ne, farmakin an yi shi ne bisa bayanan sirri na tara makamai."
Ya ce sojojin sun kwato wasu bindigogi guda uku, bindigogi kiran AK 47 guda biyu, wata nau'in bindigar guda daya, harsashi 32 da wayoyi.
Sai dai, wani rahoton jaridar Vanguard ya shaida cewa, shida ne aka kashe tare da wni soja daya.
Legit